Makalu

Macce mai yaudara a soyayya

 • Allah ya kawo mu wata zamani wacce ke tafiya da salsala daban-daban akowani bangare na rayuwa. Idan muka yi dubi a bangaren soyayya tsakanin mace da namiji, a yau yana da wuya a duk kwarewarka a soyya ko neman aure ka iya gane namiji ko mace mai yaudara sakamakon yanda zuciya ta saje wajen sajewa da ababan kelkelin rayuwa. Mace ko namiji kan iya yin halin ‘hankaka mai da dan wani naka’ ta hanyar aron kaya  ko daukar haya. Kamar da shima namiji yake iya sa abokinsa shiga na manyan mutane yaje neman masa aure, alhalin yaudararta zai yi.

  A sakonmu na yau, na yi kokari zakulo wasu daga cikin siffofin da hanyoyin gane mace mayaudariya da illolinsu. Gasunan kamar haka:

  Siffofin mace mayaudariya

  1. Daukaka kai da kai, ma’ana jiji da kai da kokarin nuna ita wayeyyiyace.
  2. Alakantar da kanta da wasu muhimman abubuwa da ake yayi yayin da take Magana. Misali nuna kusancinta da wani mai kudi, dan unguwarsu, makwabcinsu, mijin yarta ko wani ficeccen dan siyasa.
  3. Karfin hali wajensa manyan atamfa, ‘yan kune, warwaro, takallama ko rike wayar salula mai tsada.
  4. Sayan abin da ake yayi ko ta halin ka-ka, ko yin aro, haya, bashi ko sata a dakin saurayi ko gidan buki.
  5. Kwarewa fagen roko cikin hikima
  6. Shiga bokaye ko malamai don nasarar zama kan tubalin data gina rayuwarta
  7. Kallon karancin wayewa ga wadanta suka tsaya iya matsayinsu.
  8. Yin samaruka daban-daban don dorawa kowa hidimar da zai rika mata.
  9. Kaskanta abin da ta samu a matsayin ba komi bane.
  10. Gindaya sharuda ga manemanta

  Wasu daga cikin hanyoyin gane mace mayaudariya

  1. Yin binciken asalinta (idan kaima ba mayaudari bane)
  2. Son yin samaruka masu hawa motoci irin na zamani.
  3. Son yin kawance da ‘ya’yan manya.
  4. Son ziyartar dangi masu kudi kawai, don maida gidajensu adireshinta.
  5. Son afi ganinta daga cikin taron maza ko mata.
  6. Yin iko cikin kalamanta ko nunawa a fuska yayin da take waya a cikin mutane.
  7. Kauracewa zance aure duk lokacin da aka tinkareta da shi.

  Ga kadan daga cikin illolin  mace mayaudariya

  1. Takan kaskantar da iyayenta musamman in basu da abin duniya
  2. Tana sara mijin aure yayin ta bukaci auren
  3. Tana rasa ragowar imaninta sakamakon harka da bokaye
  4. Tana shiga mummunar walakanci koda ta yi aure.
  5. Asalin halittarta na iya durkushewa sakamakon shafeshafe.
  6. Tana zubarda kimar iyayenta.
  7. Akarshe takan yi mummunar karshe.

  HATTARA DAI IYAYE MATA…! Za a iya duba: Alacewar mace ta madigo da sauransu.

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Sat at 12:17 PM

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All