Makalu

Dolaki Karambana (ci gaban labari na biyu)

 • Ku danna nan don karanta farkon labarin.

  “malam ka natsu, Alhamdulillahi tunda baka mutuba…!” daya daga cikin mutanen ya fadi haka. A nan take na yi wani kukan kura na mike tsaye kafin waninsu ya kamani na diba da gudu cikin firgita da rudewa. Ban ankaraba ashe na doshi cikin makabarta ne maimakon na bi hanyar da zan yi waje.

  Me zan sake ji? Kafata ta burme cikin wani kabari na kuma ji na taka jikin gawa, nan na fadi ina ihu ina wayyo na mutu. Bayan wadannan bayin Allah sun kawo min dauki, suka tafi dani cikin gari. Anan ne nake ganin cewa ina wani kauye ne da bansan ina ne ba. Labarin da suka bani shine, sun tsinceni ne tamkar gawa a cikin daji, sun kuma bani tabbacin kwanan keso nayi shiyasa suka zaci na mutu. Anan nima na basu labarina. Suka jajantamin, suka shawarceni na kwana biyu don na yi jinya kafin ranar kasuwan kauyensu ta zagayo don samun  mota. Bayan haka akwai wani da ake kira Kaka Mudi shima zai je gari sai mu tafi tare.

  Sati na guda, na saba da mutane dayawa musamman Kaka Mudi, don yafi kowa tabbatar da cewa na amsa sunana na Karanbana.

  Ranan ina cikin dakin bukkana sai na ji hayaniyan mutane,  ashe akwai suna matan mai unguwa ta haihu yau sati ni ban sani ba. Nan take na fita, kuma gani sai dogon jumfa da mutannen suka bani ba wando, tun randa suka tononi daga kabari.

  Ina fita kuwa naga jama’a sun hadu, saidai al’adarsu ta zama sabanin tamu. Don su maza da mata na zuwa taron radin suna. Haka na lallaba na shiga cikin taron ina tsuru-tsuru da ido kamar wanda aka ba tallar hayaki. Bayan wasu lokuta aka fitar da dabino za’a raba. Nayi firit nace nima zan raba. Ba a ja daniba  na nado bakin rigar jumfata ta gaba aka zubamin, na nade na doshi mutane. Daga can sai ina ji ana cewa, ‘malam gabanka…!’ ‘Gabanka malam!’ Ni kuma sai na ce zanbasu ‘kar kudamu!’ Na doshi nan na doshi can. Ashe ni bansaniba na daga jumfana tsiraicin gabana na bayyane. Ana ta cewa ‘Dolaki Karanbana, gabanka,’ ni kuma ina cewa, ‘zan basu karku damu.’

  Ina dosan gefen mata, duk suka watse da gudu. Daga can wani ya dosoni a guje yana cewa, ‘kai nace gabanka kana watsa matan mutane’. Da ganin yanda ya dosoni sai na zati irin masu yin warwasunan ne kamar dadai na sani a garinmu. Sai na doshi cikin taron matan nima da gudu. Awannan rana an samu mata da suka karye. Mai unguwa yasa aka min dauri huhun goro aka kaini gabansa…. 

  Kuna iya karanta ci gaban labarin a nan

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Nakasar Zuci

  Posted Dec 7

  "Ki tafi gidanku na sake ki!" Runtse idanu na yi jin sautin muryar Adamu a kaina, yana furta kalaman da suka kusan sanya ni haihuwar cikin da ke jikina. Da sauri na dago jajayen idanuwana da suka gajiya da kuka na sauke a saitin sa. Wani irin tashin hankali da ciwon r...

 • Duk mace na bukatar sanin wadannan abubuwa guda 6 kafin ta yi aure

  Posted Nov 29

  Aure abu ne mai matukar muhimmanci a rayuwar mutum don ya zamo cikar mutuntaka ta dan adam. Allah madaukakin sarki ya halicci mata daga jikin mazaje domin su matan su zama natsuwa a gare su, ya kuma sanya soyayya da shakuwa a tsakanin wadannan jinsin guda biyu.  A...

 • Ko kun san adadin yawan nutrients da jikinku ke bukata?

  Posted Nov 24

  Samun abinci mai kyau da kara lafiya, wato good nutrition, ya dace ya zamo daya daga cikin burin kowani dan adam da ke raye.  Ya kasance mun san adadin yawan abinci mai kyau da jikkunanmu ke bukata, sannan mun san addadin yadda ya kamata mu rinka motsa jikinmu, kum...

 • Yadda ake hada buttered chicken

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a fannin girke-girkenmu na Bakandamiya. A yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada buttered chicken. Abubuwan hadawa Kaza Ginger and garlic paste (citta da tafarnuwa)  Albasa Yoghurt Butter Fresh cream ...

 • Yadda ake hada papaya drink

  Posted Nov 22

  Assalamu alaikum barka da sake saduwa a cikin shirin Bakandamiya a yau insha Allahu zamu gabatar da shirin yadda za ki hada natural papaya drink Abubuwan hadawa Papaya (gwanda) Sugar Ruwa Zuma (optional) Yadda ake hadawa Farko za ki yanka gwanda ki cire ma...

 • Alamomi 8 da za ki gane cewa namiji da gaske yake

  Posted Nov 22

  So wani irin yanayi ne da kan sa mutum ya tsinci kansa a cikin wani hali na daban. Sai dai mi? Abu ne shi mai dadi a kuma gefe guda abu ne mai matukar ban tsoro. Duk da kasancewar sa hakan bai zama abin ƙyama ga mutane ba. Da yawa kan rungume shi da hannun biyu. A gefe...

View All