Makalu

Featured Create an Ad

Yadda ake hada spring chin-chin

 • Assalamu Alaikum. Barkan mu da warhaka. Ayau na sake zuwa mana da sabuwar makala ta girke-girke wacce ciki za mu koyi yadda ake soya spring chin-chin.

  Abubuwan hadawa

  1. Flour (4 cups)
  2. Baking powder (1 teaspoon)
  3. Butter (125grms)
  4. Mangyada
  5. Gishiri (1 teaspoon)

  Yadda ake hadawa

  1. Za ki zuba flour a cikin bowl sannan ki saka sugar da baking powder dinki, har ila yau, ki fasa kwai daya ki saka.
  2. Sai a zuba butter a murza flour a hankali ana kara ruwa har ta hade.
  3. Sai a dan ajiye ta na mintina
  4. Sai ki yi amfani da injimin taliya ki fitar da chin-chin din ki sai ki soya har sai ya yi golden brown. Idan baki da injimin kuma sai ki yi rolling flat ki saka ribbon cutter ko pizza cutter ki yanka su straight kanana sosai, sai a soya.

  Kuna na iya duba sauran girke-girkenmu, kamar yadda ake hada KFC chicken ko kuma yadda ake hada egg masala.

MAKALU DA DUMI-DUMIN SU

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Bakwai

  Posted Thu at 8:47 PM

  Ku latsa nan don karanta babi na shida. Karima ta yi 'yar gajeriyar dariya tana mai gyara zamanta sosai, kafin ta janye mayafinta ta ajiye kan gadon tare da duban Sakinah ta fara magana da faɗin. "Ka da ki yi min mummunar fahimta, ba fa tashi tsaye na zuwa wajen malam...

 • Ma'aurata: Babi na Biyar

  Posted Mon at 5:34 AM

  Ku latsa nan don karanta babi na hudu. Malam Hasan d'ane ga K'asim su biyu ne rak ga iyayansu shi da d'an uwan haihuwarsa Husaini 'yan Asalin jahar Katsina ne suna zaune a Magamar Jibiya dukkaninsu suna da ilimin Arabik dana boko Alhaji Hasan yana zaune a cikin ka...

 • Akwai Illah: Babi na Biyu

  Posted Feb 20

  Ku latsa nan don karanta babi na daya. Hannunsa sanye da ankwa, doguwar kaca manne ta k'asa ya iso k'afarsa da ke zagaye da wata ankwar. Da k'yar yake ajiye takunsa, idanunsa na lumshewa, leb'b'ansa ya bushe. Fatar jikinsa da ya kasance bak'i mai haske ya disashe, yay...

 • Mijina Wukar Fiɗar Cikina: Babi na Daya

  Posted Feb 19

  Karfin karar albarusai da suka fito daga bututun bingigan nan da ake kira AK47 ne suka fiddamu daga nisan barci da muke yi. “My dear, meka faruwa?” matata Muhibbat ta tambaya cikin ruɗani. Kafin na buɗe baki nace wani abu, tuni wasu albarusai sun tarwasa gi...

 • Bayanan farko-farko da dalibi ya kamata ya sani game da karanta physics

  Posted Feb 17

  Ita kalmar physics ta samo asali ne daga kalmar “physis” wanda a turance za’a ce physis means nature and natural characteristics. Masana sun yi defining physics a harshen Turanci kamar haka “physics is a branch of science that/which deals with th...

 • Jini Baya Maganin Kishirwa: Babi na Shida

  Posted Feb 13

  Ku latsa nan don karanta babi na biyar. Tuni sun kammala haɗe kayan sha-shin Sakinah, masu aikin har sun zo sun fara aikinsu, Kamal tuni ya jima da fita, suna tsaka da haɗe na ɗakunan Hajiya suka tsinkayi sallama a tsakar gida. "Assalamu alaikum". Ita ce kalmar da ta...

View All